Hukuncin kashe- kai

Egypt's Dar Al-Ifta

Hukuncin kashe- kai

Tambaya

Mene ne hukuncin kashe- kai?

Amsa

Kashe- kai haramun ne a shari’ar Musulunci, hasali ma yana cikin manyan zunubai; Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Kada ku kashe kawunanku, lallai Allah mai tsananin jinkai ne a gare ku), Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Duk wanda ya kashe kansa da wani abu, to da abin za a yi masa azaba a ranar alkiyama) [al- Bukhari da Muslim], sai dai duk da cewa wanda ya kashe- kansa ya aikata babban laifi, amma dai wannan babban laifin ba zai sanya a sifanta shi da kafirci, ya fitar da shi daga addini ba, a’a za a yi masa wanka a yi masa likkafani, a kuma yi masa sallah a binne shi a makabartan Musulmai; a kuma roka masa rahama da gafara, amma da duk da haka bai kamata a dauki wannan babban laifin a matsayin ba a bakin- komai yake ba, kada kuma a yi ta bai wa masu aikata shi mafita, wajibi ne duk wanda ya ji wata alama da za ta kais hi ga haka, irin masu fama da ikti’ab, su yi gaggawar zuwa su ga likita domin su taimaka masu da magani har su fita daga cikin wannan yanayi.

Share this:

Related Fatwas