Sadaka magudaniya

Egypt's Dar Al-Ifta

Sadaka magudaniya

Tambaya

Wadansu hanyoyi ne ake bayar da sadaka magudaniya?

Amsa

Fuskokin alheri da ya inganta a sanya dukiya aciki saboda Allah mai gudana su na da yawan gaske, ita sadaka maigudana tana daga cikin nagartattun ayyuka, kuma tana daga cikin ayyukan neman kusancin bawa zuwa ga Allah dasu, kuma irin hakan yana amfanar da mamaci bayan rasuwar mutum, Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam yace: (Idan mutum ya mutu ayyukansa na yankewa in banda abubuwa uku, akwai sadaka mai gudana, akwai ilimi da ake amfana da shi, akwai yaro nagari mai yi masa addu’a) Muslim.

Ita dai sadaka mai gudana ita ce kamar wakafi, an shardanta akan abinda aka sanyashi wakafi ya kasance a bayyane yake ta inda za a iya sayar dashi, tare da amfanuwa da shi tare da wanzuwarsa, kuma kar ya zama akwai hakkin wani ciki, hakanan ya halasta a sanya wakafi na kudi da abinci kamar yanda wasu sashen malamai su tafi akan haka.

Share this:

Related Fatwas