Tsarin iyali
Tambaya
Wasu irin hanyoyin tsarin haihuwa ne shari’a ta halatta?
Amsa
Ya halatta a yi amfani da duk wata hanya da likitoci suka amince da ita wajen tsarin iyali, ta yanda hanyar za ta cika dukan ka’idoji da sharuddan da likitoci suka sanya, wadanda za su hana cutar da lafiya, su kuma samar da maslahar da ake fatan samu idan an yi amfani da wannan hanya; kuma hakan ya kasance bayan amincewar duka ma’aurata biyu. Lallai kafin wannan lokaci malaman Fiqihun Musulunci sun halatta azalo a matsayin hanyar hana daukan ciki; ganin cewa azalo ne hanyar da aka sani a wannan lokaci, kai tun ma kafin zamanin Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), abin bai takaita akansa kawai ba, Allah Mai girma da daukaka shi ne cikakken masani.