Barin Sallah

Egypt's Dar Al-Ifta

Barin Sallah

Tambaya

Mene ne hukuncin mai barin sallah?

Amsa

Sallah ita ce ginshikin addini, daya ce daga cikin rukunnan Musulunci, Allah mai girma da buwaya ya ba mu umurni yinta; mai girma da daukaka ya ce: (Ku tsayar da sallah ku kuma bayar da zakka) [al- Bakra: 43], sallah tana da wani matsayi na musamman a Musulunci, an iyakance mata rukunnai, da lokuta, da yanda ake fara ta da yanda ake kare ta, bai kuma halatta a jinkirta ta ga barin lokacinta ba sai idan akwai uzuri na shari’a, kuma barin yin sallah saboda kasala ba shi cikin uzurorin shari’a, duk wanda ya bar ta saboda kasala da nauyin jiki, to wajibi ne mu yi ta yi masa nasiha, muna masu kwadaitar da shi ladan da zai samu idan ya kiyaye ta, mu kuma yi haka cikin hikima da wa’azi mai kyau, kaman yanda Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa’azi mai kyau) [an- Nahli: 125], mu kuma cigaba da hakuri akan haka komin tsawon lokaci; kaman yanda Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ka bai wa iyalanka umurnin yin sallah, ka kuma cigaba da hakuri da juriya wajen ba su wannan umurnin) [Taha: 132], muna kuma yi masa addu’a Allah ya shiryatar da shi, ya kuma haskaka zuciyarsa ya yi masa biyayya, Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Lallai Allah yana amsa addu’ar da mutum yake yi wa dan uwansa a boye, akwai mala’ika a wurin kansa yana cewa: “amin” a duk sanda ya yi masa addu’ar alhairi, kai ma kana da irin abin da ka roka masa), Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Addu’ar da aka fi saurin amsawa ita ce: wanda ba ya kusa, ya yi wa wanda ba ya kusa); lallai yana cikin aikata sabo, yana kuma matukar bukatar wanda zai kama hannunsa ya fitar da shi daga cikin tabo ne, ba wanda zai sanya ya debe kauna ga barin tuba ba, balle ya zama mai taimaka masa akan bata da dagewa akanta tamkar shaidan.

Allah Madaukakin Sarki shi ne masani.

Share this:

Related Fatwas