Jinkirta sallah
Tambaya
Mene ne hukuncin jinkirta sallar Issha’i har zuwa tsakiyar dare?
Amsa
Abin da yazo cikin hadisai tabbatattu daga Annabi S.A.W. shi ne fifita jinkirta sallar Issha’i daga farkonta zuwa daya bisa uku na dare ko kuma rabin daren, daga cikin wadan nan hadisan akwai wanda Tirmizi ya ruwaito daga Zaid bin Khalid Al’juhani Allah ya kara masa yarda daga Annabi S.A.W. ya ce: “In banda ina gudun tsanantawa al’ummata ba da na umurce su da yin asuwaki yayin kowace sallah, sannan da na jinkirta yin sallah Issha’i zuwa kashi daya cikin uku na dare”
Wannan shi ke kasancewa ga wanda ya san cewa idan ya jinkirta yin sallar barci ko kasala ba za su rinjaye shi ba, saboda kulawa da lokacin kiran sallah ko kuma yin ikama a masallaci, idan ba haka ba to ya wajaba ya gaggauta gabatar da ita a farkon lokacinta.