Isra’i da Mi’iraji

Egypt's Dar Al-Ifta

Isra’i da Mi’iraji

Tambaya

Menene hakikanin mu’ajizar isra’i da mi’iraji, menene dalilin faruwar hakan, kuma menene hukuncin wanda yake inkarin hakan?

Amsa

Tafiyar isra’i da mi’iraji ta kasance gaskiya, kuma ta kasance ne ga Manzon Allah S.A.W. kuma ta faru ne a fadake wanda hakan ke kasancewa  kyauta daga Ubangijinsa mai girma da buwaya, sai darajarsa ta kara daukaka, inda yayi tafiya - a fadake – a cikin dare daga Masallacin Makkah zuwa Masallacin Al’aksa, inda anan ya jagoranci Mala’iku da Annabawa –Alaihim salam - sallah a cikin masallacin,  sannan daga nan aka tafi da shi sama - Sallahu Alaihi wa Alihi wa sallama -  a fadake daga masallacin Al’aksa zuwa sammai bakwai, daga nan kuma ya wuce har zuwa kololuwar sama.

Daga nan aka bijirowa da Manzon Allah S.A.W. a cikin wannan daren mai albarka manyan ayoyi, daga ciki akwai Aljanna, don yaga irin tanajin da Allah ya yiwa ‘yan Aljanna na sakamako da ni’imomi domin ya yiwa masu tsoron Allah albishir da ita, haka nan an nuna masa-  Sallahu Alaihi wa Alihi wa sallam - gidan wuta, don yaga irin azabar da Allah ya tanadawa ma’abotanta na daga azaba mai radadi, don yiwa kafirai da mushirikai gargadi da ita.

A wannan lokacin ne Allah ya farlantawa Annabi S.A.W. salloli guda biyar tare da al’ummarsa cikin yini da dare, wanda ladaddakinsu suka kai na salloli guda hamsin, sannan Allah ya kebance Annabi S.A.W. da baiwar da wani cikin ‘yan’uwansa Annaba – Tsira da amincin Allah ya tabbata a garesu baki daya – bai rabauta da hakan ba.

Hakika Al’kur’ani mai girma da sunnar Annabi S.A.W. sun yi bayani akan hakan, hakanan sahabbai sunyi ijima’i akan hakan, don haka babu dalilin da zai sa wani ya sauka daga kan wannan layin, sannan babu wanda ya yi inkarin hakan sai dai karkatattu masu jiji da kai.

Share this:

Related Fatwas