Rusa daman shugabancin shugaban ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..)
Tambaya
Waɗanne ginshiƙai ne suka yi sanadiyyar rushewar shifofin shugabanci ga shugaban ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da Boko Haram..)?
Amsa
Lallai shugaban ƙungiyan nan mai aikata laifuffuka –wadda ta lulluɓe kanta da mayafin addini- ba shugaba ba ne da yake da halacci, ko inganci ba, hasali ma bai halatta ya zama shugaba da za a amince masa ba kwata- kwata.
Saboda duk abin da aka gina shi akan jahilci da rashin sani, sam ma bai halatta ya faru ba, rashin sanin nan shi ne sanadin rushewarsa tun daga tushe, to ina kuma a ce akan shugaban da ake da’awar cewa shi ne Halifan Musulunci, amma kuma an jahilci sanin wane ne shi, kuma mene ne asalinsa, yaya tarihinsa yake, balle a yi masa mubaya’a akan haka!.
Lallai duk Halifan da wannan ne sifarsa, to sam ma bai halatta a kira shi da Halifa ba; ya fi kusa da ya zama shugaban ƙungiyar ta’addanci ta sirri da take aikata laifuffuka, wadda ba ta da wata dangantaka da Shari’ar Musulunci ta kusa ko ta nesa, hasali ma ba ruwan Musulunci da shi.
Lallai samar da halifanci yana da sharuɗɗa, waɗanda dole ne a same su, idan dai har ana son ya zama halatacce, a cikin manyan waɗannan sharuɗɗa akwai: sharaɗin gina halifancin akan cikakken sanin wanda za a bai wa wannan halifancin, wanda alhaki ne a gaban Allah, da a gaban mutane.
Lallai malamai masana Fiƙihu sun sharɗanta cewa: dole ne ya zama adali a cikin tarihin rayuwarsa, ya kuma zama ya kai matakin yin ijtihadi wajen sanin hukunce- hukuncen sababbin abubuwan da suke faruwa, ya zama lafiyayye, duka waɗannan sharuɗɗa ba a san komai game da su a tare da shugaban ƙungiyar ISIS ba.