Abin da ƙungiyar ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da BH..) suke yi wa mata
Tambaya
Shin abin da ƙungiyar ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da BH..) suke yi wa mata yana cikin karantarwar Musulunci?
Amsa
Ƙungiyar ISIS (da ‘yan uwanta irinsu: ISWAP da BH..) suna yi wa mace mu’amala ta ƙololuwar rashin tausayi da mugunta, hasali ma sukan lulluɓe wannan mu’amala na rashin tausayi da suke yi wa mace da Shari’ar Musulunci, ƙungiyar ISIS a shekarun baya- bayan nan ta fitar da dokoki a wannan sashe, inda suka bayyana cewa shekarun aurar da ‘yan mata shi ne shekaru tara! Kuma wai iyakan shekarun da mace za ta yi tana neman ilimi shi ne shekaru goma sha biyar, ƙungiyar ta bayar da umurnin yi wa ma dukan mata kaciya tun daga shekaru goma sha ɗaya har zuwa shekaru arba’in da shida, inda suka yi watsi da bayanai na ilimin likitanci, sun kuma hana duk wani aiki na gyaran halitta, kuma wai duk wasu wuraren aikin gyara jiki –kaman yanda suka faɗa- aiki ne na shaiɗan, ƙungiyar ta dage akan cewa rawar da mace za ta taka bayan ta yi aure shi ne ta zauna a gida kada kowa ya ganta, babu buƙatar ta yi ta kai- komo domin samin ilimi da shahadu, a yunƙurin ƙungiyar na samun hanyoyin shigar kuɗi ne ta samar da kasuwar sayar da bayi, inda ake sayar da mata da sunan (ƙwarƙwarori)!