Kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi t...

Egypt's Dar Al-Ifta

Kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi tare da fahimtarsu ga jahadi a Musulunci.

Tambaya

Yanda kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi suka juya ma’anar  jahadi a Musulunci?

Amsa

Kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi sun juya ma’anar jahadi a Musulunci, inda suka cire ma’anar daga yalwatacciyar ma’anarta wanda yake nufin matsa kaimi da kokari wurin yakan sha’awa da son rai domin neman yardan Allah Madaukakin Sarki, tare da takaita ma’anar da kuntata ta, wanda yake kirkirarre ne, kuma mai gauraye da tsaurarawa da yin ta’addanci da kisa da rushe rushe kai tsaye zuwa ga kubutattaun mutane da ake zaman lafiya da su, Musulminsu da wadansun su. Na’am gaskiya ne ya inganta a shari’a a sanya lafazin jahadi a matsayin ma’anar yaki, misalin hakan fadin Allah Madaukakin Sarki: (Ya kai Annabi ka yaki kafirai da munafukai ka tsananta wurin yakarsu) [At-tahrim :9]. Sai dai hakan ba ya kasancewa sai da wasu sharudda na musamman, kuma masu yawan, kuma an shar’anta yin jahadi ne domin kare kai daga ta’addancin ‘yan ta’adda da wuce gona da irinsu kawai, tare da hani kan wuce iyakan abin da aka yi wa Musulmai, za mu fahimci haka ne a fadin Allah Madaukakin Sarki: (Ku yaki wadanda suke yakarku saboda daukaka kalmar Allah, amma kada ku yi ta’addanci) [Al-bakra: 190], Idan har aka samu nasarar tabbatar da kare kai daga abokan gaba, to ma’anar jahadi a wannan bigiren abun hani ne, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Idan suka karkata zuwa ga zaman lafiya, to ku ma ku karkata zuwa ga hakan) [Al-anfal: 61], saboda haka ma’anar jahadi bisa wannan fahimtar zai cigaba da kasancewa da wanzuwa kuma farilla ne akan kowane Musulmi, kuma ba ya gushewa akansa sai fa idan taklifanci ya sauka daga kansa, a dalilin haka ne aka ambace shi da babban jahadi.

Share this:

Related Fatwas