Bambanci tsakanin ma’anar jahadi da...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bambanci tsakanin ma’anar jahadi da yaki a Musulunci

Tambaya

Mene ne Bambancin da yake tsakanin ma’anar jahadi da yaki a Musulunci?

Amsa

Jahadi  FisabilillaHi a Musulunci yana da ma’ana mai yalwa wanda ya saba wa ma’anar yaki, shi jahadi FisabilillaHi yana nufin matsa kaimi da kokari wurin yakan rai da son zuciya da kuma shedan; saboda neman yardan Allah Madaukakin Sarki, Allah Mai girma yana cewa: (Wadanda suka yi jahadi saboda mu lallai za mu shiryatar da su zuwa ga tafarkinmu) [Al- ankabut: 69], a bisa wannan kofar, za mu iya daukar ma’anar jahadi a cikin shari’a a matsayin sashen wasu nau’uka na yaki, wato dai kamar yakan masu kai hari bisa manufar kare kai daga cutarwarsu, daga ciki akwai yakar bata-gari, hakan ma na daga cikin nau’ukan jahadi, don haka jahadi a wannan kuntatacciyar ma’anar nasa, to asalinsa shi ne “fardu kifaya” idan wasu suka mike da shi, to ya fadi akan sauran mutane, shi ma kuma yana da nasa sharuddan na kashin kai wanda malamai suka ambata, wanda ba ya halasta face sai da wadancan sharuddan, sabanin jahadi wanda yake dauke da yalwatacciyar ma’ana, shi yakan kasance farilla ne akan kowane mukallafi, daga cikin yakoka akwai wanda bai inganta a ambace shi da sunan jahadi FisabilillaHi ba, wato shi ne duk jahadin da ya rasa wani sharadi daga cikin sharuddansa na shari’a, kamar dai rashin samun umurnin waliyul amri (shugaba), ko kuma idan aka fare shi ga wadanda ba su kawo wa kowa hari, wato wadanda ake zaune lafiya da su, kamar dai irin jahadin da kungiyoyin ‘yan ta’adda suke kiran da a yi.

 

Share this:

Related Fatwas