Kalmomin (Darul kufri) kasar kafirc...

Egypt's Dar Al-Ifta

Kalmomin (Darul kufri) kasar kafirci da (Darul Islam) kasar Musulunci

Tambaya

Shin ma’anar kalmomin (Darul kufri) kasar kafirci da (Darul Islam) kasar Musulunci tana nan tana aiki? Mene ne dalilan da suka sanya samar da wadannan sunayen a tarihi?

Amsa

Babu bukatar cigaba da amfani da ma’anar kalmomin (Darul kufri) kasar kafirci da (Darul Islam) kasar Musulunci a wannan zamanin, dalilin haka kuwa shi ne irin dangantaka da dokoki da yarjejeniyoyi da suke tsakanin kasa da kasa a zamanance, wanda za mu iya cewa dukkan kasashen duniya sun aminta da su, kamar yanda kuma bayyanar wasu lamura su ma sun taimaka wurin disashe hanyoyin amfani da irin wadannan kalmomi, kamar dai irinsu: “kasashe masu ‘yanci” da “kasa daya al’umma daya” ta inda ya kasance nuna wariya tsakanin mutane a bangaren hakkokinsu da wajiban da suke kansu bisa bambancin addini, ko kabila, ko launi, ko dangane, laifi ne da ake hukunta duk wanda ya taka su a dokokin kasashen duniya, sabanin yanda yanayi ake a baya, kasa da karni guda, nuna bambanci ya kasance wani sashe ne da wayewar mutanen duniya baki daya, hakan ya sa malaman fikihu suka samar da kalmomi irinsu: kalmomin (Darul kufri) kasar kafirci da (Darul Islam) kasar Musulunci, hakika Musulunci ya yi kira a mafi yawan nassoshin shari’a daga Al’kur’ani Mai girma da Sunnar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) a kan a yi watsi da irin wannan bambancin a kuma daina amfani da shi, a bisa wannan dalilin ne ya sa malaman Musulunci suka kasance na sahun farko wurin aminta da wadancan  dokoki da yarjejeniyoyi a lokacin da aka samu sauyin lamura.

Share this:

Related Fatwas