Kafa kungiyoyi da suke adawa da tsari na bai daya da suke kira zuwa ga fito na fito da Daula
Tambaya
Shin ya halasta a samar da kungiyoyi da ke adawa da tsari na bai daya da suke kira zuwa ga fito na fito da Daula?
Amsa
Bai halasta a samar da kungiyoyi da suke adawa da tsari na bai daya da suke kira zuwa ga fito na fito da Daula ba, wannan yana daga cikin tsari na Musulunci, -Rashin halascin hakan– saboda hakan na bude kofar hada fada da barna a bayan kasa, tare da cusa ruhin damuwa da tsoro a zukatan mutane, tare da yada kiyayyar juna da rarrabuwa a tsakanin mutane, uwa uba hakan na iya zama sanadin rasa da tsaro da zaman lafiya a cikin al’umma, to wannan tuzarci ne ga manufofin shari’a bayyananniya, wacce da dalilinta aka aiko da Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam), domin Allah Madaukakin Sarki yana cewa: (Idan har munafukai da wadanda suke da ciwon a zukatansu da masu yada jita jita a Madina ba su hanu daga barin munanan ayyukansu ba lallai sai mun kunyata maka su sannan kuma ba za su kara makwaftakanka a wurin zama ba sai dan kadan. Su ababen la’anta ne a duk inda aka same su a kama su a karkashe matukar karkashewa) [Al-ahzab: 60-61]. Saboda haka ita Daula ita ce mutane na hakika bisa ma’anar Sunna mai tsarki, haka nan samar da wata kungiya ta daban domin ta yi adawa da wannan Daular to warewa ne daga cikinta. Hakika Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Taimakon Allah yana tare da jama’a, duk wanda ya ware daga jama’a to ya ware kansa zuwa wuta) [Tirmizi]. Don haka ya kamata mutane su rinka yin taimakekeniya a tsakaninsu bisa da’a da tsoron Allah, tare da watsar da sabo da gaba da rashin dena yin biyayya, ko bin kiraye- kirayen rabuwar kai da wasu masu sabo suke yi.