Ma’anar “al-Hakimiyyah”

Egypt's Dar Al-Ifta

Ma’anar “al-Hakimiyyah”

Tambaya

Wane ne wanda ya fara amfani da ma’anar Hakimiyya, kuma ta yaya wannan ma’anar ta sauya salo a wannan zamanin?

Amsa

Mutum na farko da ya fara amfani da kalmar Hakimiyya su ne Hawarijawa a zamanin halifancin Imamu Aliyu dan Abu Dalib (Alla ya kara masa yarda) yayin da suka raya cewa Imamu Aliyu ya shugabantar da wasu mutane a cikin addinin Allah, to wannan –a wurinsu– kafirci ne, domin babu mai hukunci sai Allah, sai suka kafa hujja da fadin Allah Madaukakin Sarki: (Shi hukunci na Allah ne) [Yusuf: 40], Hakika Imamu Aliyu ya mayar musu da martani inda ya ce: “Wannan kalmar gaskiya ce amma bata ake nufi da ita” [Muslim]. Sannan daga baya ma’anar Hakimiya ya kara samun ta-gomashi –wurin ma’ana– a hannun masu tsattsauran ra’ayi kamar irin su Maududy da Sayyid Khudub bisa ma’anar “Yin hukuncin Allah”, ko “kadaita yin hukunci” ta inda suka sanya kadaita Hakimiyya a matsayin wani kashi daga kashe kashen kadaita Allah, sai ya zama ya saba wa hakan ya sabawa rukuni na tauhidi, daga haka kuma sai mutum ya zama ya fita daga Musulunci kenan, suna nufin “Hakimiyyar Allah” zartar da hukuncinsa, inda suka raya cewa dukkan kundayen tsarin mulki na kasashen Musulmai da dokokinsu sun sabawa shari’ar Musulunci saboda ba Allah ne ya sanya su ba, mutum ne dan Adam, amma a zahirin gaskiya dukkan mazhabobi na fikihu da dokoki baki dayansu dan Adam ne ya samar da su, domin ba su kasance ba face kwafi ne na hukunce hukuncen fikihu.

Share this:

Related Fatwas