Hakikanin kungiyoyin ‘yan ta’adda

Egypt's Dar Al-Ifta

Hakikanin kungiyoyin ‘yan ta’adda

Tambaya

Ta yaya malaman musulunci suke ganin hakikanin kungiyoyin ‘yan ta’adda masu wuce gona da iri?

Amsa

Lallai dukkan kungiyoyin ‘yan ta’adda sunyi tarayya bisa jahiltar addinin Allah da kuma karfin hali wurin kafirta musulmai da halasta jininsu, da zaluntar bayin Allah, wanda hakan ya kai ga kallonsu a matsayin ‘yan sako ne na abokan gaba da suke amfani da su wurin wargaza al’umma daga tsakiyarsu, saboda manhajin wadannan ‘yan ta’addan masu kafirta mutane – Da suka yi nesa da jama’a – yana karkata ne zuwa ga kambaba sabani da rarrabuwar kai da fadada gaba a tsakanin musulmai, hakanan wannan manhajin nasu yana karkatar da al’umma zuwa ga warware koyarwar Addinin Musulunci tare da bata masa suna inda hakan yake baiwa makiya musulunci daman a yi suka gareshi, musamman ta sashen da musulmai suke da natsuwa dashi.

Wadannan kungiyoyin na ‘yan ta’adda – Tun farkon kafuwarsu – ba su da aiki sai cusa tsoro a zukatan mutane ta hanya mai muni da tsoratarwa, manufar hakan shine bayyana karfin ikon da suke da shi, tare da aikawa da sakonsu zuwa ga mafi yawan mutane domin tankwarasu da kuma tsoratar da su da firgita duk wanda zai yi tunanin tunkararsu, hakanan kuma wannan salon na janyo musu sabbin magoya baya cikin masu raunin zuciya a bisa hawa hanya wacce take karkatacciya mai kaiwa ga ayyukan laifi domin shiga cikin rundunarsu da suke yakar mutane dasu, hakanan wannan kungiyar kan bi salon yin kisa da dauri da kisan kare dangi ga duk wanda ya sabawa ra’ayinsu ko fahimtarsu.

Share this:

Related Fatwas