Bin matakai na daga cikin manufofin...

Egypt's Dar Al-Ifta

Bin matakai na daga cikin manufofin shari’a mafi girma.

Tambaya

Ta yaya kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi ke bijirar da musulunci ga wadanda ba musulmai ba?

Amsa

Kungiyoyin masu kafirta musulmai su na dogara da manhajin da ba madaidaici ba wurin bayyana musulunci a matsayin addinin ta’addanci da sata da warwaso da kuma kisa, wanda hakan yana iya fadawa duk wanda bai bi tsarinsu da suke bayyanwa ba da sunan musulunci, wanda ke daidai da tunaninsu, wannan manhajin karkatacce ne kuma haramtacce ne a shari’a, hakika manzon Allah SallalaHu AlaiHi wa AliHi wasallam ya bayyana manhaji tsayayye domin bayyana musulunci da kuma yada shi a tsakanin mutane, wanda hakan shine manhaji tsayayye wanda ya ginu akan matakai daban daban da kuma saukakawa da kiyaye dukiya da rayuka da mutumtaka, don haka sai muka samu umurnin manzon Allah SallalaHu AlaiHi wa AliHi wasallam ga Mu’az bin Jabal da ya lura da wadannan abubuwan, tare da iyakance gwargwadon makura bisa halin mutanen da ya aike shi zuwa garesu na mutanen Yamen, inda suka kasance mabiyan littafi ne ana son kiransu zuwa ga musulunci daga addinin da suke bi, wanda iliminsa ya tabbatu a tsakaninsu, zuwa ga addinin musulunci sabo, sai manzon Allah SallalaHu AlaiHi wa AliHi wasallam ya iyakance masa abubuwan da zai yi amfani dasu wurin kiran da zaiyi musu zuwa ga Allah, cewa da mai zai fara kuma ta yaya zai gabatar sai ya ce masa:(Lallai kai zaka je wurin wasu mutane na Ahlul kitab, to ka kira su zuwa shaidawa da La ilaha Illallah sannan kuma ni Manzon Allah ne,- a wata ruwayar kuma ya ce: ya zama farkon abinda zaka fara kiransu zuwa gareshi shine yiwa Allah Mai girma da Buwaya bauta, - Idan sun yi biyayya to ka sanar da su cewa Allah ya farlanta musu salloli Biyar a cikin yini da dare, idan suka yi biyayya ga hakan, to sai ka sanar da su cewa Allah ya farlanta musu bayar da zakka wanda za a rinka amsa daga mawadatansu domin a baiwa mabukatunsu, idan har suka yi biyayya ga hakan to na horeka da amsar dukiyarsu, kaji tsoron addu’ar wanda aka zalunta saboda babu shamaki tsakaninta da Allah) Anyi ittifaki akansa.

To wanna shi ake kira da bi a sannu sanu ko bin matakai wurin gamsar da mai karbar zance ta matakai na shari’a, inda suke kafa hujja da dalilai masu yawa da suka zo cikin Al’Kur’ani da Sunna, hakika nassoshi na shari’a daga Al’Kur’ani da Sunna sunyi nuni akan bin manhaji matsakaici da maidaidaici wanda shine manhajin Ubangiji tsayayye.

Share this:

Related Fatwas