Hanyoyin yaduwan tsattsauran ra’ayi...

Egypt's Dar Al-Ifta

Hanyoyin yaduwan tsattsauran ra’ayi.

Tambaya

Wasu ayyuka ne kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi ke dogaro da su wurin yada tunaninsu da ayyukansu na ta’addanci?

Amsa

Kungiyoyin ‘yan ta’adda su na dogara akan wasu ayyuka da suke ingiza su ga kara yaduwa da fadada ayyukansu na laifuka, bangare na musamman akan haka shi ne bangaren manufa da tunani, don haka kungiyoyin ‘yan ta’adda su na yin kokarin baiwa wani abu na daban muhimmanci wanda bai yi kasa – a wurin hadari – da yada manufofin ta’addanci ba, wato wannan abu kuwa shi ne kafofin sadarwa dake hada alaka tsakanin mutane, saboda irin wadannan kafofin suna taka rawa sosai wurin yada manufofin ‘yan ta’adda ba tare da wani wahala ko kashe makudan kudade ba, a wasu lokutan yin amfani da wadannan kafofin wurin yada manufansu na zama mafi hadari daga aikata ta’addancin a zahiri.

Yawaitar hanyoyin amfani da wadannan kafofin da ‘yan ta’adda suke amfani da su, da yawa sukan kasance matattara ne na masu aikata laifuffuka, don haka wannan ke zama wani babban tarnaki wurin yakar manufofin kungoyoyi masu tsattsauran ra’ayi, saboda yin kawance tsakanin kungiyoyin ‘yan ta’adda da kuma kungiyoyin masu aikata manyan laifuffuka na taimakawa musu tsattsauran ra‘ayi wurin samun kariya da samun  kudaden shiga masu yawa, a wani lokacin ma hakan na taimakawa wurin horar da sabbin shiga kungiyoyin da saukaka zurga zurgansu zuwa wurare daban daban, daga muhimman kungiyoyin masu aikata laifuffulan da ‘yan ta’adda  suke yin hadaka da su sun hada da:

Kungiyoyin masu safarar kwayoyi, kungiyoyin masu satan kayayyakin tarihi ko saye da sayarwa, kungiyoyin masu yin kaura ba bisa ka’aida ba.

Masu kira zuwa ga goyawa ra’ayin ta’addanci baya sun samu nasarar cimma burinsu sosai na amfani da wannan salon musamman yada manufarsu da kuma samun masu ra’ayin shiga kungiyoyinsu da samun horo akan haka, tare da samun nasarar magana kai tsaye da matasan da suke da sha’awar shiga cikin kungiyoyin nasu, hakika wannan hanyar ta taimaka sosai wurin jan ra’ayin mutane da yawan gaske daga ko’ina cikin fadin duniya domin shiga cikin kungiyoyin nasu.

Share this:

Related Fatwas