Abubuwan da su ke ingiza mai tsatts...

Egypt's Dar Al-Ifta

Abubuwan da su ke ingiza mai tsattsauran ra’ayi aikata laifukansa (1).

Tambaya

Wasu abubuwa ne mafiya muhimmanci wurin ingiza mutum zuwa ga ayyukan ta’addanci masu tsauri?

Amsa

Ana lura da cewa rashin samun karsashi a jiki da kuma jin kaskanci a zuci suna daga cikin abubuwan da ke ingiza ran mutum zuwa ga aikata laifi.

Rashin samun karkashi a jiki saboda damuwa yana daga cikin nazarurruka mafiya hadari da kuma karbuwa wurin fassara hakikanin tsattsauran ra’ayi, wannan rashin karsashin na zuwa ne sakamakon hauhawan burace buracen da mutum ke son cimmawa a ransa, amma sai dai saboda yanayin da shi mutum yake ciki yakan kasa samun cimma burinsa kamar yanda yake fata, wanda hakan ke ingiza shi zuwa ga kyamar kowa da kowa.

A bisa haka ne wannan kyamar ke sanya mutum ya canza ya rinka aikata munanan ayyuka, daga haka sai yiwuwar shiga cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda ya zama mai sauki gare shi, kuma zabi gare shi a karshe.

Jin kaskanci a zuciya ko kuma abin da ake kira a wurin malaman sanin halayyar dan adam da (Dumauta):

Hakika wadansu nazararruka sun gudana akan halin jin kyama ko damuwar zuci na daya daga cikin abubuwan da suke haifar da tsattsauran ra’ayi, domin kuwa irin wancan halin na haifar da rashin jin natsuwa a rai, saboda haka sai mutum ya fara neman hanyoyin samun natsuwa a wurin irin wadancan kungiyoyin na ‘yan ta’adda, a wannan lokacin sai ya fara jin karfi a ransa da kuma natsuwa.

Lallai makamancin irin wannan mutumin da yake fama da irin wannan cutar ba abin da yake fama da shi idan ba neman karin karfi ba, sai muga yana ta kokarin killace kansa domin gudanar da rayuwarsa ta hanyar matsa kaimi wurin mayar da martini mai zafi ba tare da hakuri ba domin cimma burinsa ta kowace hanya ba tare da la’akari da mutane ba.

Share this:

Related Fatwas