Karanta Alkur’ani a cikin jama’a
Tambaya
Mene ne hukuncin karanta Alkur’ani a cikin jama’a?
Amsa
Karanta Alkur’ani cikin tsararriyar jama’a, ba tare da takura, ko dauke hankali a lokacin karatu, ko karantarwa –kaman yanda aka saba a majalisan karantar da Alkur’ani mai girma a wasu daga cikin masallatai, ko makaratun allo- abu ne da shari’a ta halatta, hasali ma yana cikin zikiri a cikin jama’a, wanda masu yinsa suke samun lada, sannan kuma ta hanyarsa ake isa zuwa ga manufar karantarwa, da bayar da gudummuwa wajen isar da Alkur’ani.
Hadisi ya zo daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) game da yanda yake tsara majalisa karantarwa, ta yanda ba za a takura wa juna, Kaman yanda ya zo a Hadisin Abu Hazim al- Tammar, daga al- Bayadhiyyu (Allah ya kara yarda da shi), cewa lallai Manzon Allah ya fito ya ga mutane suna sallah, sun daga muryoyinsu wajen karatu, sai ya ce: (Lallai mai sallah yana ganawa ne da Ubangijinsa mai girma da buwaya, saboda haka ya kula da abin da zai gana da shi, kada wani daga cikinku ya daga murya wajen karatun Alkur’ani akan muryar wani) [Imam Malik a cikin al- Muwadda].