Maganar cewa: (Babu addini cikin si...

Egypt's Dar Al-Ifta

Maganar cewa: (Babu addini cikin siyasa, kuma babu siyasa a cikin addini)

Tambaya

Shin maganar cewa: (Babu addini cikin siyasa, kuma babu siyasa a cikin addini) gaskiya ce?

Amsa

Idan ya kasance muna magana ne akan yin siyasa a jam’iyyance, to wannan zancen gaskiya ne, ya kamata jam’iyyun siyasa su nesanta kansu daga wasu alamomi na addini cikin lamuran yaƙin neman zaɓensu kawai domin bambanta kansu da sauran jam’iyyu, idan ba haka ba, to wannan zai kasance wani nau’i ne na ci da addini, kuma ya zama dalilin zargin sauran jam’iyyu da rashin kishin addini, to irin wannan zai jawo fitina a tsakanin al’ummar ƙasa ɗaya.

To irin wannan shi ya jefa ƙungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi yin taho mu-gama da al’umma bayan sun shiga harkokin siyasa, yana da kyau malamin addini ya nesanta kansa daga shiga siyasa irinta jam’iyya don ya zama na kowa, sannan ya cigaba da ilmantar da mutane kyawawan abubuwan da za su tabbatar da abubuwa masu alfanu ga kowa da kowa a matsayinsa na malamin addini.

Amma siyasa a ma’anarta na gama gari to tana nufin kulawa da lamuran ƙasashe da kuma mutanen da ke zaune cikinsu da wajensu, a bisa la’akari da wannan to ba zai yiwu a raba siyasa da addini ba, domin suna tafiya ne kafaɗa da kafaɗa domin tabbatar da amfanin mutane, kamar yanda madogarar shari’a take wakiltar da siyasa – ta wannan fuskar – domin gina wani rufi wanda ba za a yarda a ƙetare shi ba wurin hidimta wa ɗan Adam, shin wannan hidimar ta fuskar shari’a ce ko kuma ta fuskar hidimta wa al’umma, ko ta wasu fuskokin daban.

Share this:

Related Fatwas