Ya rasu yana da wadata amma bai yi ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Ya rasu yana da wadata amma bai yi aikin Hajji ba

Tambaya

Mene ne hukuncin wanda ya rasu da wadatarsa amma bai yi aikin Hajji ba?

Amsa

Mustahabi ne mutumin da yake da iko na kudi da lafiya ya yi gaggawar zuwa aikin Hajji, ya kuma halatta ya jinkirta, idan yana da zato mai rinjaye na cewa zai cigaba da zama cikin lafiya, da samun dama a bayan lokacin, amma idan zaton nasa ya fi karkata akan zai rasu sakamakon kamuwarsa da wata cuta, ko tsufa, to wajibi ne ya gaggauta sauke faralin da yake a kansa

Idan yana da ikon gabatar da aikin Hajji, ya kuma rasu ba tare da ya yi ba: to ko dai ya zama ya yi wasiyya game da Hajjin, kuma yana da kudin da ya bari gado; to a nan wajibi ne a yi masa Hajji daga sulusin abin da ya bari. Ko kuma ya zama ya rasu ba tare da ya bar wasiyya ba, amma kuma ya bar kudin da za a gada; to a nan ba dole ne magadansu su yi masa aikin Hajji ba, an dai so su yi masa, haka ma mutumin da ya rasu ba tare da ya yi wasiyya a yi masa aikin Hajji ba, sannan ma bai bar kudin da za a gada da zai isa a cikin sulusinsa ba.

Share this:

Related Fatwas