Yin tasarrufi a kudin bashin da a ...

Egypt's Dar Al-Ifta

Yin tasarrufi a kudin bashin da a san mai asalin kudin ba.

Tambaya

Mahaifina ya sanar da ni – kafin rasuwarsa – cewa wani mutum yana binsa bashi, hakika nayi binciken wannan mutumin amma ban sameshi ba, shin zan iya tasarrufi a cikin wannan kudin?

Amsa

Shi dai asalin wannan bashin yana cikin abinda mahaifinka ya bari, don haka za a ware shine tun kafin a raba gado, don haka sai kuyi kokari wurin neman mai wannan hakkin ko kuma magadansa, idan kuma baku samu daman isa zuwa ga mutumin ko magadansa ba to ya zama hakkin magada, har sai an samu mai hakkin domin a bashi, daga nan sai kowa cikin magadan ya dawo da kason da ya samu a farko bayan mai hakkin ya bayyana, saboda hannun karba hannun mayarwa, hakanan a shari’ance babu laifi a bayar da wannan bashi ga mutum daya, ta inda ko da mai hakkin ya bayyana to shi zai biya, kuma ya halasta ga wanda aka baiwa kudin ya juya su ta yanda yake so, amma kuma ya zama a cikin ransa wanda ke rike da kudin akwai niyyar biyan mai hakkin hakkinsa a duk lokacin da ya bayyana, idan har lokaci ya yi nisa ta kai ga cire tsammanin bayyanar mai hakkin ko kuma isa zuwa gareshi to mafi dacewa shine ayi sadaka da kudin.

Share this:

Related Fatwas