Yin barci ba tare da yin sallar Asuba ba.
Tambaya
Mene ne hukuncin yin barci ba tare yin sallar Asuba ba?
Amsa
Yana daga cikin abinda akaso a shari’ance musulmi ya gudanar da sallah a farkon lokaci, an karbo daga Abdullahi bin Mas’ud Allah ya kara masa yarda, yace: Na tambayi Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam: Wani aiki ne mafi soyuwa ga Allah? Sai yace: (yin sallah a lokacinta).
Amma dangane da wanda wata sallah ta wuceshi a lokacinta kamar saboda barci ko mantuwa ko makamancin haka to ya wajaba gareshi yayi gaggawan ramawa, hakika Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam yace: (Wanda ya manta yin wata sallah, ko yayi barci bai yita ba, to kaffaran hakan shine ya ramata idan ya tuna da ita), idan mutum yayi barci baiyi sallar asuba ba har rana ta fito, ba tare da yin ganganci ba, kuma bai farka ba saboda tsananin gajiya, to sai ya rama sallar bayan ya farka daga barci, a cikin hadisin Safwan bin Al’mu’attal Allah ya kara masa yarda yana cewa: ... bamu kasance muna tashin hae sai bayan rana ta fito, sai Annabi SallallaHu AlaiHi wa AliHi wasallam yace masa: (Idan ka farka to kayi sallarka).