Kafirci ba shi ne illar kisa ba

Egypt's Dar Al-Ifta

Kafirci ba shi ne illar kisa ba

Tambaya

Shin rashin shiga cikin addinin Musulunci dalili ne na halatta jini, da rashin ba shi kariya?

Amsa

Lallai mafi yawan malamai sun tafi akan cewa kafirce ba shi ne dalili, ko illa na kisa a cikin shari’ar Musulunci ba, ba kuma dalili ne na halatta jini ba ta kowace irin hanya, sai dai idan a yanayi na ta’addanci, babu yanda za a yi a ce addinin Musulunci ya zo ne saboda kawai Musulmai su kadai su rayu cikin aminci da zaman lafiya, hasali ma akasin haka ne, domin Musulunci ya zo ne saboda ya dasa tutar zaman lafiya da aminci tsakanin daukacin bil’adama, Musulmai su ne al’ummar da suka amsa kira, suka kuma yi imani, wadanda ba su ba kuma su ne al’ummar da ake kira, ake kuma yi masu bayani, Allah Madaukakin Sarki y ace: (Ba mu aiko ka ba sai domin ka zama rahama ga talikai) [al- Anbiya’i: 107], lallai Allah Madaukakin Sarki ya tabbatar da yiwuwar yin sabani, Allah mai girma ya ce: (Da Ubangijinka ya so da sai ya sanya daukacin mutane su zama al’umma guda daya, amma ba za su gushe ba suna sabawa da juna, sai wanda Ubangijinka ya lullube su da rahama, saboda ma haka ne ya halicce su..) [Hudu: 118- 119], haka yana cewa: (Da Ubangijinka ya so da daukacin wadanda suke a doron kasa sun yi imani) [Yunus: 99], Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Idan wani mutum ya aminta da wani mutum akan rayuwarsa, sannan ya kashe shi, to kuwa ba- ni ba- makashin, koda kuwa wanda aka kashe kafiri ne) [al- Dayalisiy da al- Baihakiy], a wata ruwaya kuma: (Lallai makashin ba shi ba zimmar Allah), to ta yaya zai yi bara’a da wanda ya kashe kafiri, da a ce kafirci dalili ne na halatta jini?!.

Share this:

Related Fatwas