Wakilci wajen sallar Istihara

Egypt's Dar Al-Ifta

Wakilci wajen sallar Istihara

Tambaya

Shin ya halatta  yi wakilci wajen sallar Istihara?

Amsa

Abin da daukacin malamai suka hadu akansa game da sallar istihara shi ne sunna ce; an so duk wanda ya kuduri aniyar yin wani abu bai kuma san karshen wannan abu yaya zai kasance ba, bai san cewa alhairi aikata shi, ko barinsa ba, to ya yi sallar istihara, wadda raka’a biyu ce ba ta farilla ba, sannan bayan ya kamala sai ya yi wannan addu’a da aka ruwaito daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) “Allahumma inniy astakhiruka bi ilmika, wa astaqdirula bi qudratila, wa as’aluka min fadhlikal azimi..” har zuwa karshen Hadisi [al- Bukhari].

Malamai masana fikihu a mazhabobin malikiyya da shafi’iyya sun halatta mutum ya wakilci waninsa wajen sallar istihara, kaman uwa ta yi a maimakon danta, ko aboki ya yi a maimakon abokinsa; saboda yin haka taimakekeniya ne wajen aikin alhairi; saboda maganar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) cewa: (Duk wanda zai iya amfanar dan uwansa a cikinku to ya amfane shi) [Muslim].

Share this:

Related Fatwas