Sallar Istikhara

Egypt's Dar Al-Ifta

Sallar Istikhara

Tambaya

Shin ya halatta a yi sallar Istikhara a lokutan da aka karhanta yin sallah?

Amsa

Makruhi ne a gabatar da sallar istikhara a lokutan da aka karhanta yin salloli a cikinsu, wadanda lokuta ne guda biyar, wadanda ba a sallah a cikinsu, sai idan sallar tana da dalili: bayan sallar asubahi har zuwa hodowar rana, da lokacin hodowarta har zuwa lokacin da za ta cika da daga gwargwadon baka, wato minti ashirin bayan fitowar rana, da kuma lokacin da za ta gama cikanta a tsakiya, har zuwa lokacin da za ta dan karkata, ma’ana kafin kiran sallar azuhur da mintuna hudu, da bayan sallar la’asar har zuwa fadawar rana, da lokacin fadawar har zuwa ta gama fadawa duka. Wannan ne hukuncin jamhur din malaman fikihu na mazhabobin Hanafiyya, da Malikiyya, da Shafi’iyya, amma idan mutum ya yi sallah a lokacin ya halatta, sai dai makruhi ne, a wurin mazhabar Hanbaliyya ne kawai ta halatta ba tare da karaha ba.

 

Share this:

Related Fatwas