Sallar mutum daya.
Tambaya
Shin sallar wanda ya tsaya a bayan sahun mutane shi kadai ta inganta?
Amsa
Malaman fikihu sun yi sabani akan ingancin sallar mutumin da ya kasance shi kadai ne a bayan sahun matane, inda Hanafiyya da Malikiyya da Shafi’iyya su ka tafi akan cewa idan mai sallah ya tsaya a bayan sahu saboda ba zai iya samun shiga cikin sahun ba saboda jinkiri ko matsatsi ko wani abu makamancin haka, to sallarsa ta inganta, ba tare da wani abu na karhanci ba, amma idan mutum ya tsaya a bayan sahu tare da cewa zai iya shiga sahun, to sallarsa ta inganta tare da karhanci, sannan kuma mutum zai samu ladan jam’i, domin ya yi sallarsa cikin jam’i.
Su kuwa malaman Hambaliyya sun tafi akan cewa, idan mutum ya yi cikakkiyar raka’a daya a cikin wannan yanayin to sallarsa batacciya ce.
Domin haka, sallar wanda ya yi a bayan sahu, tare da samun ikon shiga cikin sahu amma bai shiga ba, to sallar ta inganta tare da karhanci, kuma hakan ba zai hana shi samun ladan jam’i ba, akan so mutum ya yi kokarin shiga cikin sahu ko ya yiwa wani ishara a hankali da ya dan dawo daga baya domin su hada wani sahun sabo.