Sallar Tuba (Salatut Tauba)

Egypt's Dar Al-Ifta

Sallar Tuba (Salatut Tauba)

Tambaya

Mene ne hukuncin Sallar Tuba (Salatut Tauba)? Kuma yaushe ake yinta?

Amsa

An ruwaito Hadisi daga Sayyiduna Abubakar (Allah ya kara yarda da shi) ya ce: Na ji Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (Babu wani mutum da zai aikata zunubi, sannan ya tashi ya yi alwalla, sannan ya yi sallah, sannan ya nemi gafarar Allah face ya gafarta masa), sannan ya karanta wannan ayar: (Su ne wadanda idan sun aikata alfasha, ko suka zalunci kawunansu, sai su tuna Allah, su kuma nemi a gafarta masu zunubansu) [Ali Imran: 135] [al- Tirmiziy]. Wannan Hadisin ya bayyana halaccin sallar tuba, kuma malamai sun hadu akan cewa mustahabiya ce, an so a duk sanda Musulmi ya aikata sabo da ya yi alwalla, ya kuma kyautata alwallar, sannan ya yi sallah raka’a biyu, ya yi iya bakin iyawarsa a ciki, ya hallarto da zuciyarsa, ya ji tsoron Allah Madaukaki, sannan ya nemi gafarar Allah , Allah cikin karamcinsa zai gafarta masa, kuma dole ne ya cika sharuddan tuba da suka hada da: nadama akan abin da ya aikata na sabo, ya kuma kudurci aniyar rashin sake aikatawa, idan kuma sabo yana da dangantaka da hakkin dan Adam ne, ya fara da mayar masa da hakkinsa. Allah shi ne masani.

Share this:

Related Fatwas