Sallar mara lafiya da azuminsa

Egypt's Dar Al-Ifta

Sallar mara lafiya da azuminsa

Tambaya

Mene ne hukuncin sallah da azumin mara lafiyar da cutar take yi masa tasiri a ikon da yake da shi da motsinsa?

Amsa

Idan za a sha wahala wajen gabatar da sallolin farali, to Allah mai girma da dauka ya saukake wa mara lafiya akan ya gabatar da su daidai da ikon da yake da shi, gwargwadon iyawarsa a tsaye, ko a zaune, ko a shingide, ko a rigingine, yana mai yi nuni a ruku’u da sujada, idan hakan ma ya gagara, zai iya yin nunin da ido ko da gira, ko a zuciya –sallah takan fadi akansa a mazhabar Hanafiyya- lallai rahamar Allah mai girma da daukaka tana da fadi ga kowa.

Share this:

Related Fatwas