Jarraba da rashin lafiya yana kankare zunubai
Tambaya
Shin jarraba da rashin lafiya yana kankare zunubai?
Amsa
Lallai Allah mai girma da buwaya ya yi wa bayinsa baiwa ta hanyar da ya sanya hakurin da suke yi akan duk wani abu da yake samunsu –ba tare da sun nuna rashin amincewa ba- a matsayin dalili daga cikin dalilan da suka kankare zunubai da kura- kuran da suka yi, Sayyiduna Abuhuraira (Allah ya kara yarda da shi) ya ruwaito Hadisi daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Babu wata gajiya, ko rashin lafiya, ko bakin ciki, ko damuwa, ko wata cutarwa da take samun Musulmi, kai har sukar kaya, face Allah ya kankare masa kura- kuran da ya aikata da abinda ya same shi) [al- Bukhari].
Sayyiduna Anas Bn Malik (Allah ya kara yarda da shi) ya ruwaito Hadisi cewa Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya shiga wajen gaisar da wani Balaraben kauye da ba shi da lafiya, sai ya same shi cikin damuwa, sai ya ce masa: (Kaffara ce da tsarkakewa) [Ahmad]. Allah yana kulawa da mara lafiya sakamakon hakurin da ya yi akan abin da ya same shi, da kuma yarda da hukuncin Allah Madaukakin Sarki akansa, al’amarinsa akan haka dukansa alhairi ne. Allah shi ne Madaukaki, kuma masani.