Jarrabawar rashin lafiya yana kanka...

Egypt's Dar Al-Ifta

Jarrabawar rashin lafiya yana kankare zunubai

Tambaya

Shin jarrabawar rashin lafiya yana kankare zunubai da kura-kurai?

Amsa

Lallai Allah mai girma da buwaya ya yi wa bayinsa baiwa, inda ya sanya hukurin da suke yi akan cutar da ta same su, ba tare da korafi ko raki ba, ya zama sanadin kankare masu zunubansu da kurakurensu, Abuhuraira (Allah ya kara yarda da shi) ya ruwaito Hadisi daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Babu wani rashin lafiya, ko gajiya, ko damuwa, ko bakin- ciki, ko cutarwa, ko tsananin yanayi, kai har sukar kayar da za ta sami mumini face Allah ya kankare masa kura- kuransa saboda su) [al- Bukhari]

An ruwaito Hadisi daga Anas Bn Malik (Allah ya kara yarda da shi) cewa: Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya shiga wurin wani Balarabe ya gashe shi a lokacin da yake cikin damuwa, sai ya ce: (Kaffara ce da kankare zunabai) [Ahmad a cikin Musnad], Allah ya bayar da kulawa ta musamman ga mara lafiya, sakamakon hakurin da yi akan abin da ya same shi, da kuma yarda da abin da Allah ya kadara masa, al’amarinsa duka alhairi ne, Allah shi ne masani.

 

Share this:

Related Fatwas