Shakka akan abin da aka yi bakace akansa
Tambaya
Mutum ne ya yi bakace, sannan ya yi shakka akan abin da ya yi bakacen akansa, mene ne hukuncinsa?
Amsa
Wanda ya yi bakace, sannan ya yi shakka, ko ya manta abin da ya yi bakace da shi; shin sallah ne, ko azumi, ko sadaka, ko wani abu irin haka; to lallai zayyi iya bakin kokarinsa akan abin da zatonsa ya fi rinjaya, sai ya yi shi, idan kuma ya yi iya bakin kokarinsa bai iya isa zuwa ga sanin nau’in abin da ya yi bakace da shi, to kaffara ce ta wajaba akansa; domin yin shakka akan abin da aka yi bakace akansa, daidai yake da ba a ayyana ba, ganin cewa ya gaza wajen ayyana makamancin abin da ya yi bakace da shi.
Allah shi ne masani.