Algushi a cikin kayan da aka yi yar...

Egypt's Dar Al-Ifta

Algushi a cikin kayan da aka yi yarjejeniyar a kawo

Tambaya

Mene ne hukuncin Algushi a cikin kayan da aka yi yarjejeniyar a kawo a cikin harkar kwangila?

Amsa

Algushi a cikin kayan da aka yi yarjejeniyar kawowa ta hanyar harkar kwangila haramun ne a shari’ar Musulunci, yana cikin cin dukiyoyin mutane ta hanyar zalunci. Lallai Musulunci ya haramta algushi da yaudara, Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Duk wanda ya yi mana algushi ba shi daga cikinmu) al- Dairamiy ya ruwaito, asalinsa yana cikin sahihul Bukhari da Sahihu Muslim.

Haka ma Allah ya umurci Musulmai da su yi gaskiya, su kuma kasance tare da masu gaskiya, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi imani ku ji tsoron Allah, ku kuma kasance tare da masu gaskiya) [at- Tauba: 119].

Haka ma Musulunci ya wajabta cika alkawari da sharudda, muddin dai bai saba wa shari’a, ko asalin kasuwancin ba, Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Musulmai suna nan akan sharuddan da suka yi da juna, banda sharadin da ya haramta halal, ko ya halatta haram) [ald Daru Kudniy].

Share this:

Related Fatwas