Yanda akeyi a yayin da makabarta ya...

Egypt's Dar Al-Ifta

Yanda akeyi a yayin da makabarta ya cika

Tambaya

Mene ne matsayin makabartan da ya cika da gawarwaki, kuma me ya kamata muyi bayan haka?

Amsa

A cikin yanayi na lalura da tsananin bukata – kamar dai yanda ake samu makabartu da yawa-  to:

Ya halasta ayi zagaye na biyu na kaburburan bisa niyyar tattara kasusuwan mamatan wuri daya a cikinsa.

Hakanan ya halasta a rufe mamacin da ya dade da makari na turbaya ko duwatsu ta yanda ba za atabi jikinsa ba, sannan wannan makarin da aka sanya za a rufeshi da turbaya, daga nan sai a rufe sabon mamacin.

Hakanan ya halasta a tsara wani abu mai dauke da kasusuwan mamata, daga baya sai a sake rufesu gaba daya a wannan makabartan.

Hakan na kasancewa ne matukar dai lalura ta tilasta hakan.

Duka fa wannan yana kasancewa ne da sharadi na girmama mamatan da suke kwance ko kuma girmama burabusan kasusuwansu da suka rage, domin shi mutum ana girmamashi bayan rasuwarsa kamar yanda ake girmamashi da ransa.

Share this:

Related Fatwas