Yanda ake yin sallar janaza.
Tambaya
Ya ake ake yin sallar janaza?
Amsa
Ita dai sallar janaza ana yin kabbara hudu ne, mai yin sallar zai karanta fatiha bayan kabbarar farko, bayan kabbara ta biyu kuma sai ya karanta kashin karshe na tahiya, irin dai wanda yake yi a lokacin sallah, ai: Daga farkon da yake cewa: (Allahumma salli ala sayyidna Muhammad....) har zuwa karshen tahiyan, sannan bayan kabbata ta uku sai ya karanta addu’a ga mamacin na nema masa gafara, a bayan kabbara ta hudu kuma sai mai yin sallar janaza ya yi wa kansa addu’a tare da sauran al’ummar musulmai, sannan sai ya yi sallama biyu, a dama da hagunsa.