Ayoyin amfani da takobi da ayoyin a...

Egypt's Dar Al-Ifta

Ayoyin amfani da takobi da ayoyin afuwa da kawar da kai

Tambaya

Shin Ayoyin  amfani da takobi sun shafe ayoyin afuwa da kawar da kai?

Amsa

Ayoyin amfani da takobi ba su shafe ayoyin afuwa da kawar da kai ba, daga cikin ayoyin amfani da takobi akwai inda Allah Madaukakin Sarki yake cewa: (Ku kashe mushirikan a duk inda kuka same su) [At-tauba : 5], daga cikin ayoyin afuwa kuma akwai inda Allah Madaukakin Sarki yake cewa: (Ka yi riko da afuwa ka yi umurni da abu mai kyau sannan ka kawar da kanka daga jahilai) [Al-a’araf: 199],  saboda haka ayoyin amfani da takubba ana amfani da su wurin kare kai, haka nan ayoyin afuwa ana amfani da su a sauran yanayin da aka tsinci kai, kuma babu cin karo da juna a tsakaninsu bare har a ce wata ayar ta shafe wata daga cikinsu, domin malaman usulul fikihi sun shardanta rashin yiwuwar haduwar dalilai biyu a wuri daya, domin kuwa Annabi Muhammadu (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi amfani da wadannan ayoyin guda biyu da makamantarsu a lokuta mabanbanta, domin ya yi sulhu da mushirikai inda ya kulla sulhun zaman lafiya a Hudaibiyya, wannan kuma yana zuwa ne bayan ya yake su a Badar da Uhudu da Khandak domin kare kai, sannan ya bude garin Makkah yayin da Kuraishawa suka warware nasu alkawarin zaman lafiyar, sannan ya yi musu afuwa kamar yanda ya zo cikin Hadisin (Ku tafi ku abun sakewa) shahararre, malamai sun yi ittifaki kan cewa al’amarin yaki da zaman lafiya abin bari ne ga shugaba da tsarin siyasarsa wacce za ta kare martabar al’ummarsa baki daya.

Share this:

Related Fatwas