Asalin dangantaka tsakanin mai mulk...

Egypt's Dar Al-Ifta

Asalin dangantaka tsakanin mai mulki da wadanda ake mulka.

Tambaya

Mene ne asalin dangantaka da take tsakanin mai mulki da wadanda ake mulka?

Amsa

Asalin dangantaka tsakanin mai mulki da wanda ake mulka shi ne yarjejeniyar da take tsakaninsu, wato dai shi ne sauraro da biyayya daga wanda ake mulka zuwa ga wanda yake mulki, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ya ku wadanda kuka yi imani ku yi biyayya ga Allah ku yi biyayya ga Manzon Allah da shugabannin dake cikinku) [An-nisa’i: 59], Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Ku yi sauraro ku yi biyayya, koda an shugabantar muku da bawa dan Habasha ne, wanda kai ka ce kansa zabiba ne saboda tamukewa) [Bukhari]. Daga bangaren shugaba kuma ga wadanda yake shugabanta ya wajaba ya yi shugabancinsa bisa abin da al’ummarsa suke bukata na bai daya da ke cigaban manufofin shari’a, kamar dai tsayar da adalci da kawar da zalunci tare da kiyaye addini, da tabbatar da tsaro da zaman lafiyar al’umma daga hadarurrkan waje da na cikin gida, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Ya kai Dauda lallai mu mun sanyaka ka zama halifa a bayan kasa don haka ka yi hukunci a tsakanin mutane da adalci kada ka bi don zuciya) [Saad: 26]. Sai dai fa Musulunci bai sanya yin adalcin shugaba ga talakawansa a madadin yi masa biyayya ba, domin in ba haka ba, to ai lamuran al’umma za su rikice kenan, don haka ne ma Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya yi wa al’ummarsa wasici da cewa: (Duk wanda ya ga wani abu da yake kinsa ga shugabansa to ya yi hakuri, domin duk wanda ya rabu da jama’a daidai da tuka daya, sannan ya mutu – a cikin wannan hali – to ya yi mutuwar jahiliya) [al- Bukhari da Muslim].

Share this:

Related Fatwas