Asalin dangantaka tsakanin mutane.

Egypt's Dar Al-Ifta

Asalin dangantaka tsakanin mutane.

Tambaya

Shin asalin dangantaka tsakanin mutane a Musulunci zaman lafiya ne, ko yaki kamar yanda kungiyoyin ta’adda suke ikirari?

Amsa

Amsa:

Asalin dangantakar da take tsakanin mutane a Musulunci shi ne aminci “zaman lafiya” ba yaki ba, kamar dai yanda kungiyoyi masu tsattsauran ra’ayi suke ikirari, hakika Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Idan suka kaurace muku ba su yake ku ba suka mika muku hannun zaman lafiya, to Allah bai sanya muku wata mafaka na yakarsu ba) [An-nisa’i: 90], a zahiri wannan ayar ta yi nuni ne akan cewa an shar’anta  yaki cikin Musulunci ne domin mayar da martani akan ‘yan ta’adda kawai, a lokacin da kafirai suka nesanci yaki, to bai halasta ga Musulmi su kai musu hari ba, ya inganta daga Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) cewa: (Cikakken Musulmi shi ne wanda mutane suka kubuta daga harshensa da hannunsa, mumini cikakke kuma shi ne wanda mutane suka amintar masa da jininsu da dukiyarsu) [An-Nasa’i]. Hakika Allah Madaukakin Sarki shi ne wanda ya zabi sunan Musulunci ga addininsa, hakikanin adawa makadaiciya a Musulunci wacce take cigaba da wanzuwa a mafi yawan lokuta ita ce Musulmi ya rinka yi wa kansa adawa mai yawan aikata laifuka, sannan kuma adawar Musulmi da shedan, dalilin gabatar da rai akan shedan shi ne kusancinta da mutum tare da lizimtarshi – shedan-  ga shi mutum  a dukkan halaye da tsanantan hakan gare shi, tare da haka yin gwaji da matsa kaimi rai kan iya zama mai taimakawa wurin yin biyayya, amma shedan yakan kauracewa mutum da zaran ya nemi tsarin Allah da ga shi.

Share this:

Related Fatwas