Ilimin sanin halayyar mutane.

Egypt's Dar Al-Ifta

Ilimin sanin halayyar mutane.

Tambaya

Mene ne nazarin ilimin sanin halayyar dan Adam akan halayyar mai tsattsauran ra’ayi da kuma yanayin tunaninsa?

Amsa

A lokuta da daman gaske mai tsattsauran ra’ayi yana ganin kansa a matsayin kebantacce ne daga cikin al’umma, yana ganin wannan kasancewa na musamman din a matsayin damarsa na tsaurarawa da nuna ta’assubanci ta fuskar tunani da zafafawa wurin kamanta abubuwa ta hanyar gudanar da su, sai muga masu irin wannan fahimtar na tsanani suna aikata abubuwa bisa gwargwadon yanda tunaninsu ke basu, sai su rinka jin cewa su na daban ne a cikin mutane, sannan sukan bayyana ra’ayin da karfin gwiwa saboda suna jin cewa hakan ne kadai zai ba su kariya, ya kuma cigaba da tabbatar musu da wancan sifar da suke jin cewa sun kebanta da su a cikin al’umma.

Irin wannan jin cewa akwai fifiko ko banbanci tsakanin mai wannan ra’ayi da sauran mutane yana iya kaiwa ga samar da wani yanayi mai kama da mayar da martani a karkace ga shi wannan mutumin, ta yanda ta wannan hanyar zai rinka kokarin tabbatar da wasu abubuwa da suka saba da zahirin lamari ko yanayin da ake ciki, abin nufi anan shi ne al’ummar da shi wannan mai tsanantawar yake rayuwa a cikinta za ta iya gazawa wurin hada kanta wurin yin kan kan kan da sauran al’ummu irinta da suka samu cigaba sosai a bangaren tattalin arziki da kimiyya ko wani abu mai kama da hakan,  sai alamar da hakan yake haifarwa ya yi tasiri sakamakon tsananin bukatar al’umma wurin kamo sauran al’ummu da suka yi musu nisa ta fuskar cigaba, a daidai wannan lokacin shi kuma mai tsanantawan nan sai ya fara bayyana kansa a matsayin wani mutum na daban da kwarewarsa da sabaninsa da sauran al’umma, wanda zai nuna cewa shi mutum ne na musamman a tsakanin mutane.

Share this:

Related Fatwas