Bibiyan aibobin mutane

Egypt's Dar Al-Ifta

Bibiyan aibobin mutane

Tambaya

Shin bibiyan kura- kuren mutane da tuntubensu da kokarin saninsu haramun ne? Yaya za a yi a tuba akan haka?

Amsa

Wannan bibiyan al’aurar mutane ne, kuma sam bai halatta a rinka bibiyan al’aura da aibobin mutane ba; saboda bibiyar aibobin mutane dabi’a ce mara kyau, hakan yana cikin al’amurran da aka haramta, wadanda suke dasa kiyayya a cikin zukata, suke kuma yada barna a cikin al’umma.

Wajibi ne ga duk mutumin da ya bibiyi aibobin mutane ya tuba, ya kuma koma zuwa ga Allah, ta hanyar neman afuwar da rangwame daga wadanda ya zalunta, ba tare da hakan ya zama hanya ko dalilin da zai fallasa kansa ba, in kuma ba haka ba, sai ya tuba tsakaninsa da Ubangijinsa, ya nema masu gafara, kada abin da ya same shi ya sanya ya zama yana kin mutane, ko ya rasa ganin darajarsu.

Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Duk wanda ya suturta Musulmi Allah zai suturta shi ranar alkiyama) [al- Bukhari da Muslim].

Abin da ya kamata shi ne ya shagaltu da aibobinsa, ya kuma tuba akan kura- kurensa.

Share this:

Related Fatwas