Biyan bashin mamaci

Egypt's Dar Al-Ifta

Biyan bashin mamaci

Tambaya

Shin wajibi ne magada su biya bashin wanda za su gada idan bai bar masu abin da za su biya masa bashi ba?

Amsa

Shari’ar Musulunci ta kwadaitar akan sauke nauyi da hakkoki, wanda bashi daya ne daga ciki, Allah Madaukakin Sarki ya ceL: (Yak u wadanda kuka yi imani, ku cika alkawurran da kuka dauka) [al- Ma’ida: 1], lallai shari’a mai tsarki ta bayyana wajibcin biya wa mamaci bashin da yake akansa, ana gabatar da shi akan wasiyya, da rabon gado ga magada, Allah Madaukakin Sarki ya ce: (Bayan wasicin da ya yi ko biyan bashi) [an- Nisa’i], idan kuma bai bar gadon da zai isa a biya masa bashin ba, to an so magadansa su biya masa bashin da yake akansa, su rarraba bashin a tsakaninsu, daidai da yanda suka aminta a tsakaninsu; domin hakan yana daya daga cikin manyan ma’anoni na biyayya ga mamaci, saboda maganar Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) da ya ce: (Ran mumini a rataye yake da bashin da yake akansa, har sai a biya masa).

Share this:

Related Fatwas