Yin azumi a madadin mamaci

Egypt's Dar Al-Ifta

Yin azumi a madadin mamaci

Tambaya

Mene ne hukuncin wakiltan mamaci wajen yi masa azumin da ya kubuce masa

Amsa

Abu ne da malaman fikihu gaba dayansu suka hadu akansa cewa azumi muhimmin ginshiki ne cikin ginshikan Musulunci; inda Allah ya yi wa masu azumi alkawarin samun babban lada, sai dai ta yiwu wani uzuri na shari’a ya bijiro wa mutum ya hana shi yin azumi, irinsu: rashin lafiya, da tafiya, da ala’da, ko biki da suma, idan mai azumi ya sha azumi saboda wani uzuri da ake fatan zai gushe, amma wannan uzurin ya cigaba har zuwa rasuwarsa, to malamai sun hadu akan cewa babu bukatar wani ya yi masa azumi a maimakonsa, ba kuma za a yi masa fidiya ba, ba kuma shi da wani laifi, domin bai yi sakaci da shi ba. amma idan uzurin ya gushe, ya kuma sami daman rama azumin da yake a kansa, amma bai yi ba saboda sakaci har ya rasu, to ya kamata magadansa su ciyar a maimakonsa a cikin sulusin dukiyar da ya bari, duk azumi a ciyar da miskini daya, idan har ya yi wasici da haka, in kuma bai yi ba, su yi masa a matsayin sadaka.

Share this:

Related Fatwas