Yada ilimin mamaci.
Tambaya
Ta yaya shari’a ta kwadaitar da yada ilimin da mamaci ya bari tare da gargadi kan boye ilimin?
Amsa
Yana daga cikin dalilai mafi girma na biyayyan magaji ga wanda yake gadonsa ya zama yana kokari wurin yada abin da ya bari na ilimi ba wai boyewa ba, so da yawa tarin ilimi yakan salwanta sakamakon rowar da magada suke da shi na yada shi ilimin, tare da katange ilimin ga shi mamacin a maimakon sauran mutane su amfana da shi, ko kuma ilimin yakan gushe sakamakon sakacin magada wurin yada ilimin tare da barinsa a yanayin da ba zai yiwu mutane su isa gareshi ba, bare har su amfana da shi, amma da ace magada sun yada ilimin ta hanyar da ya dace, sannan suka amincewa mutane su amfana da ilimin to da hakan ya zamo dalilin daukakan wanda ya rubuta ilimin tare da samun lada mai yawa wanda zai rinka zuwa ga mamacin bayan rasuwarsa.