Yada sirrikan mutane

Egypt's Dar Al-Ifta

Yada sirrikan mutane

Tambaya

Mene ne hukuncin yada sirrikan wasu mutane na daban a kafofin sadarwa na zamani.

Amsa

Bai halasta a yada sirrikan wadansu mutane na daban ba, sirrikan da mutane ba sa son duniya ta sani abin sakayawa ne, shin a kafofin sadarwa ne na zamani ko a kafafen labaru ko a wasu hanyoyin na daban, saboda sirrikan mutum abu ne na kashin kai wanda bai kamata wani ya kutsa ciki ba, hakika nassoshi na shari’a sun zo inda suka bayyana cewa sirrikan mutane amana ne bai kamata a yada ba, musamman abubuwan da ba zasu so wani ya sani ba, bai halasta ga wanda yake iya sanin sirrikan mutane ya rinka yadawa ba, tunda ba a yarda ya yada ba.

Hakanan ya haramta a yada sirrikan mutane ta hanyar fallasa bayyanansu da suke kin mutane su sansu, saboda hakan zai cutar dasu, to shi dai cutar da mutane abun zargi ne a shari’ance, hakika hani kan hakan da yin gargadi kansa yazo cikin shari’a, Allah Ta’ala ya ce: (Wadanda suke cutar da muminai maza da muminai mata ba tare da wani laifi ba to hakika sun dauki zunubi da sabo mabayyani) [Ahzab: 58]  

Share this:

Related Fatwas