Tsarkake mutane

Egypt's Dar Al-Ifta

Tsarkake mutane

Tambaya

Ta yaya za mu iya fahimtar matakin “ladabi da biyayya” a wurin kungiyoyin masu kafirta mutane da ‘yan ta’adda?

Amsa

Shi dai ladabi da biyayya ko tsarkake mutune na daga cikin abubuwa mafi hadari da ke karfafa tunanin wasu matasa masu bincike don sifantuwa da addini da bin shari’a na sau da kafa, musamman idan ya zama wadanda suke amsar ilimi a wurinsu masu irin wancan tunanin ne, masu karkata zuwa ga tunani da ta’addanci, don haka masu irin wannan karantarwar sukan rudi mutane da cewa sune masu magana da sunan shari’a, idan aka cigaba da kulla alaka tsakanin shari’a da irin wanda ya yake irin wannan karantarwar sai ya kasance ma shi ne shari’a a wurin mai karatu a wurinsa, a maimakon ya rinka fadin ra’ayinsa ko fahimtarsa a addini sai kawai ya mayar da maganarsa kawai ita ce addini, daga haka sai mai sauraronsa ya fara tsarkakesu ba tare da yasan yana hakan ba ma, ire iren wadannan mutanen sune suke saurin shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda cikin sauki ba tare da yin tunanin abin da zai kai ya komo ba, ana ganin irin haka yana daga cikin abubuwa na tarayya a manhajojin ‘yan ta’adda.

Kungiyar ‘yan’uwa musulmai ta zarce sauran kungiyoyi matsa kaimi wurin matakin “sauraro da biyayya” wanda hakan dai kamar daya ne daga cikin tsare tsaren kungiyoyi, ta yanda duk mai bin kungiyar ba shi da wani zabi da zai yi sai yin biyayya garesu, wanda irin tsarkakensun da yake yi a wurin nazari zai ciru zuwa ga tunaninsa.

Saboda haka ne ma fatawar irin wadancan mutanen ke zama daya daga cikin sinadarai masu muhimmanci sosai a wurin ‘yan ta’adda domin cimma burinsu, a duk lokacin da irin wadancan fatawowin suka yawaita to sukan karkata ne wurin tsattsauran ra’ayi, musamman fatawowin da suke zuga mutane nuna wariya da  kyamar ga wasu.

Share this:

Related Fatwas