Jinkirta ayyukan mutane

Egypt's Dar Al-Ifta

Jinkirta ayyukan mutane

Tambaya

Mene ne hukuncin jinkirta wasu ma’aikata kan ayyukan mutane ba tare da dalili ba?

Amsa

Shi ma’aikacin gwamnati shi ne dan gwadugon da ake bashi albashi a duk karshen wata, to fa shi amintacce akan aikin da yakeyi wanda aka dora alhakin hakan a wuyansa, don haka rashin gudanar da aikin nasa kamar yanda ya kamata tare da karban albashin aikin da baiyi ba akwai ha’inci a cikin abin da aka bashi amana, hakika Manzon Allah SallallaHu AlaiHi wa AliHi Wasallam ya ce: (Ayoyin munafiki guda uku ne, idan yayi Magana yayi karya, idan ya dauki alkawari ya saba, idan aka amince masa yayi ha’inci) Bukhari.

Hakanan gurgunta ayyukan mutane ko jinkirtasu ko rashin aiwatar da aikin mutane kamar yanda ya kamata to cin dukiyar mutane ne da barna, hakika an hanamu yin haka a cikin fadin Allah Ta’ala: (Ya ku wadanda kuka yi Imani kada kuci dukiyarku a tsakaninku da barna sai dai fa idan ya kasance ta hanyar kasuwanci ne da kika amince a junanku) [Nisa’i:92]

Bai kamata a jinkirta wasu ma’aikata daga yin aikin mutane ba tare da dalili ba, duk mai aikata hakan ya kamata ya tuba, domin abin da yake samu ya zama halal.  

Share this:

Related Fatwas