Hawarijawan zamani

Egypt's Dar Al-Ifta

Hawarijawan zamani

Tambaya

Shin akwai Hawarijawa a wannan zamanin?

Amsa

An ruwaito Hadisi daga Aliyu Bn Abuɗalib (Allah ya ƙara yarda da shi) ya ce: Na ji Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) yana cewa: (A ƙarshen zamani wasu jama’a masu ƙarancin shekaru za su fito, waɗanda tunaninsu na wawacin ne, suna furta kalmomin fiyayyen halitta, suna kuma karanta Alƙur’ani, amma ba ya wuce maƙogwaronsu, suna fita daga addini kaman yanda kibiya take fita daga baka, idan kun haɗu da su ku kashe su, domin akwai lada a wurin Allah ranar alƙiyama ga wanda duk ya kashe su) [al- Bukhari da Muslim]. Waɗannan wasu sifofi ne na Hawarijawa da Manzon Allah (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya bayyana, kaman yanda ya faɗa kuma za su bayyana ne a ƙarshen zamani, saboda haka duk wanda ya sifantu da waɗannan sifofi a kowane zamani ya shiga ciki, kuma babu shakka kan cewa ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi da suka bayyana a wannan zamanin irinsu ISIS da ‘yan uwanta da suka fito suna yaƙar shugabannin Musulmai da sunan tabbatar da Hakimiyyar Allah da tsayar da Shari’ar Allah, suka kuma kafirta ɗaukacin mutane, suka halatta jinin Musulmai da mutuncinsu, suka yaɗa kashe- kashe da fitintunu a cikin jama’an “La’ilaha illalLahu”, duka waɗannan suna nuna cewa lallai manhajojin Hawarijawa sun tabbata a cikin waɗansu daga cikin ƙungiyoyi a wannan zamanin, musamman ma dai ƙungiyar ISIS.

Share this:

Related Fatwas