Harkar kayan maye
Tambaya
Mene ne hukuncin kasuwancin kayan maye, mene ne kuma hatsarin haka?
Amsa
Lallai malamai sun bayyana cewa duk wani abu da yake sanya maye haramun ne, duk wani abu da yake zama dalili na rasa hankali, ko yaya yake shi ma haramun ne; abin da ya sanya har Imam al- Badrul Ainiy a cikin littafinsa “al- Binaya” (12/370) ya hakaito cewa sun yi ijma’i akan wannan haramcin, a inda ya ce: (Saboda wiwi ba ya kisa, amma dai yana gusar da hankali, yana sanya rauni, yana kuma sanya kasala, yana dauke da munanan sifofi abubuwan da zargi; akan haka gaba dayan malamai da suka zo a baya (Allah ya yi masu rahama) suka yi ijma’i akan haramcinsa gaba daya).
Kaman yanda haramun ne a sha kowane irin kayan maye, haka ma yin kasuwancisa haramun ne, lallai idan Allah mai girma ya haramta wani abu, to yana haramta sayar da shi, da cin kudinsa; saboda Hadisin da aka ruwaito daga Ibn Abbas (Allah ya kara yarda da su), cewa Annabi (SallalLahu alaiHi wa alihi wa sallam) ya ce: (Lallai idan Allah ya haramta wani abu, sai ya haramta kudinsa) [Ibn Hibban]. Kuma gaba dayan malaman fikihu a mazhabobi sun hadu akan cewa “Duk abin da zai kai zuwa ga haramun, to shi ma haramun ne”. Dokar kasar Misra ta tabbatar da cewa laifi na yin kasuwanci da kayan maye; doka mai lamba (2) a dokar kayan maye mai lamba 182 ta shekarar 1960 ta bayyana cewa: An hana kowane irin mutum ya samo, ko ya shigo, ko ya samar, ko ya mallaki, ko ya adana, ko ya sayi, ko ya sayar da kayan maye, ko ya yi sauyi da waninsa, ko ya kyautar, da kowace irin sifa ce kuwa, ko ya zama mai shiga tsakani, in banda a halayen da doka ta bayyana daidai da sharuddan da doka ta tabbatar.
Saboda haka, haramun ne yin kasuwanci da kayan maye, ko daukansu daga wani wuri zuwa wani; domin haramcin kayan maye, yana nyfin haramcin duk wata hanya ta take kai wa zuwa ga yaduwarsu.