Karkatar da kayan agaji

Egypt's Dar Al-Ifta

Karkatar da kayan agaji

Tambaya

Shin ya halasta a shari’ance a karkatar da kayan agaji zuwa wata fuskar?

Amsa

Shi dai asalin haka bai halasta ba, bai kamata a karkatar da kudi zuwa ga wani sashe da ba shi ne mai bayar da agajin ya bayar dominsa ba, sai dai fa idan an koma an tambayeshi, saboda wadanda suke raba kudin taimakon sune wakilan wanda ya bayar da kudin domin rabawa a matsayin taimako, kuma bai halasta wakilan su ketare abinda aka iyakance musu ba, matukar wasu kudade na agaji sun fito daga wuring masu kudin zuwa ga wani bangare, to bai halasta akarkatar da kudin zuwa wani sashe ba, sai dai fa idan har an koma an nemi izinin wanda ya bayar da kudin tun asali, tare da neman yardansu na bayar da kudin ga wani sashe na daban, don haka muna yin nasiha kamar haka:

Kira akan yin taimako ya kamata ya zama ya kunshi wani abu da zai iya fadada zuwa ga wasu hanyoyin na yin agaji.

Sannan kuma masu neman taimakon domin rabawa ya zama sun tace inda za su raba kudin, kuma ya zama wuri ne da yafi zama mafi tsananin bukata.

Share this:

Related Fatwas