Karantar da manya
Tambaya
Mene ne hukuncin shari’a game da karantar da manya, da yaki da jahilci?
Amsa
Karantar da manya, da yaki da jahilci al’amari ne da shari’a take so; saboda ayoyi da hadisan da suke nunu zuwa ga muhimmancin ilimi da neman ilimi, da kuma darajar malamai, shi neman ilimi bai tsaya akan wata iyaka, ko shekaru ba, babu bambanci tsakanin yara da manya, ko maza da mata wajen nemansa, kowa daidai suke wajen nemansa, lallai akwai labarai masu yawa da suke nuna cewa wasu daga cikin manyan ba su fara himma da dagewa wajen neman ilimi ba sai da girma ya kama su, ba kuma su ji kunyar cewa sun tsufa ba.