Fitar da zakka
Tambaya
Shin ya halasta a fitar da zakka a rarrabe na tsawon shekara?
Amsa
Ya halasta ga mai tambayar ya fitar da zakka a rarrabe na tsawon shekara bayan wucewar shekara akan dukiyarsa wanda yakai nisabi zuwa ga wadan da ya san sun cancanta, sannan suna bukatuwa zuwa ga zakkar domin biyan bukatunsu a kowani wata, tare da kulawa da ganin an kammala bayarwa a cikin shekarar kafin a shiga cikin wata sabuwar shekarar.